8 Nuwamba 2021 - 12:14
An Fara Rejistar ‘Yan Takara A Zaben Shugabancin Kasa A Libiya

Kwamitin koli na zaben shugaban kasa a Libiya (HNEC), ya sanar da bude rejistar ‘yan takara a zaben shugabancin kasar dana ‘yan majalisar dokoki da za’ayi a watan Disamba mai zuwa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Za’a karbi ‘yan takara a zaben shugabancin kasa a yankunan guda uku na kasar da suka hada da Tripoli babban birni, da Benghazi dake gabashi da kuma Sebha a kudanci, yayin da kuma ‘yan takara a zaben ‘yan majalisa zasu iya ajiye takardunsu a duk ofisoshin hukumar zaben kasar.

Masu son yin takara a zaben na Libiya na da daga yau Litini 8 ga wata har zuwa 22 ga watan Nuwamba domin ajiye takardun takararsu.

‘Yan takara a zaben ‘yan majalisar dokoki kuwa na da damar ajiya takardun takararsu daga ranar 8 ga wata har zuwa 17 ga watan Disamba, kamar yadda darektan hukumar ta HNEC, Imad al-Sayeh, ya sanar.

‘Yan Libiya sama da miliyan 2,8 ne daga cikin al’ummar kasar kimanin miliyan bakwai akayi rejistar zasu kada kuri’a a babban zaben kasar, wanda shi ne farko tun bayan guguwar neman sauyi da ta yi awan gaba da mulkin tsohon shugaban kasar mirigayi Mu’ammar Ghaddafi a cikin shekarar 2011.

342/